logo

HAUSA

An ceto mutane 3,000 da aka sace a arewa maso yammacin kasar

2022-06-22 10:55:20 CMG Hausa

 

Gwamnatin jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce tun daga shekarar 2019, hukumomi sun ceto mutane 3,000 da aka sace a jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ya bayyana yayin wani taron manema labarai, a cewarsa, an saki mutanen ne ta hanyar shirye-shiryen maslaha da tattaunawa da gwamnatin jihar ta aiwatar cikin shekaru 3 da suka gabata.

Jami’in ya bayyana lamarin a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin jihar ta samu a bangaren tsaro.

Ya ce kokarin gwamnatin ya haifar da kyawawan sakamako saboda jihar na samun zaman lafiya kuma ayyukan ’yan fashin daji ya ragu sosai cikin watanni 9 da suka gabata.

Ya kara da cewa, tun bayan kaddamar da shirye-shiryen, da yawa daga cikin ’yan fashin da suka tuba, sun mika wuya ga hukumomi. Kuma gwamnatin ta samar da ababen hawa da sauran kayayyakin aiki ga hukumomin tsaro domin yabawa kokarinsu na kare rayuka da kadarori a jihar. (Fa’iza Mustapha)