logo

HAUSA

Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta gabatar da nasarorin da kasar ta cimma a fannin kare hakkin dan-Adam

2022-06-21 19:01:37 CMG Hausa

Yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya gabatar da nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin kare hakkin dan-Adam, yayin taron manema labarai. Ya bayyana cewa, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, jama'ar kasar Sin sun ci moriyar 'yancin dimokiradiyya mai tarin yawa. Idan aka kwatanta da farkon kafuwar sabuwar kasar Sin, yawan kudin shiga na kowane dan kasar Sin, ya karu daga dalar Amurka 12 kacal zuwa dalar Amurka dubu 12, kuma matsakaicin tsawon rayuwa, ya karu daga shekaru 35 zuwa shekaru 77.3.

Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Amurka da Birtaniya da sauran kasashe, suna shirin kitsa wasu jita-jita na wai "kutsen siyasa" a kasashen yammacin duniya domin neman bata sunan kasar Sin a idon duniya. Kan wannan batu, Wang Wenbin ya ce, idan ana maganar kutsen siyasa, kasashe irin su Amurka da Birtaniya su ne abin ya zama musu jiki.

Wang Wenbin ya kuma yi karin haske, kan yunkurin kasar Amurka na haifar da batun tilasta rashin aikin yi a jihar Xinjiang na kasar Sin, wai da sunan sigar doka, yana mai cewa, kasar Sin tana yin Allah wadai da kakkausar murya da ma nuna adawa kan wannan batu. (Ibrahim)