logo

HAUSA

An kashe fararen hula 132 a tsakiyar Mali

2022-06-21 10:24:27 CMG Hausa

Kimanin fararen hula 132 aka kashe a wasu kauyuka uku dake yankin karkarar Bankass a tsakiyar Mali, kamar yadda wata sanarwar da gwamnatin Mali ta fitar ta bayyana.

A cewar hukumomin kasar Mali, al’ummun kauyukan Diallassagou, da Dianweli, da Deguessagou, da kuma kewayen yankunan karkarar Bankass mutane ne masu son zaman lafiya, sun gamu da harin rashin wayewa a daren 18 zuwa 19 ga watan Yuni.

A cewar sanarwar, an gano da dama daga cikin mutanen da suka kitsa kisan kiyashin, wadanda wani bangare ne na mayakan Katiba Macina na Amadou Koufa.

Gwamnatin kasar ta yi Allah wadai da kakkausar murya game da hare-haren, kuma ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin gano mutanen dake da hannu tare da gurfanar da su gaban shari’a. (Ahmad)