logo

HAUSA

Masana kimiyya sun yi amfani da kwari wajen hada kunu don yaki da matsalar karancin abinci mai gina jiki

2022-06-21 08:21:47 CMG Hausa

Masana kimiyya sun yi amfani da sinadaran dake cikin kwari, wajen sauya fasalin kunu na Afirka daga abincin da ba ya gina jiki zuwa abinci mai gina jiki mai muhimmanci, har ma ya zarce bukatun kananan abubuwan gina jiki ga jama’a.

Masu binciken da suka fito daga cibiyar nazarin kwari da muhalli ta kasa da kasa (ICIPE) dake da shalkwata a Nairobin Kenya, sun bayyana cewa, sabon abincin ya kawo sauyi a fannin samar da abinci mai gina jiki a Afirka.

Nelly Maiyo, daya daga cikin masu binciken ta ce, sun inganta gero mai yatsa tare da ingantattun sinadirai daga gyare da ake samu a Afirka da ake ci wanda aka fi sani da Scapsipedus da hatsi, wani nau’in kayan lambu na ‘yan asalin mazauna da ake nomawa a sassan nahiyar.

A cewar Maiyo, ana kiwon gyare na Afirka a fadin kasar Kenya, kuma yana da wadataccen danyen furotin da kitse, wanda ya kai kashi 57 cikin 100 da kashi 36 na nauyinsa a lokacin da ya bushe. Haka kuma, kwaron yana da wadataccen sinadarin amino acid, wasu sinadaran ma’addinai da kuma bitamin, kana kuma kashi 88 cikin 100 na wadannan sinadarai da jikin dan Adam ke narkarwa. Haka kuma, Allah ya albarkaci tsiron na amaranth da bitamin C da pro-vitamin A, da iron, da zinc da calcium masu tarin yawa.

Galibi ana hada kunun Afirka ne da dangin hatsi mai kama da maiwa da hatsi mai yatsu, wadanda ke da wadataccen carbohydrates, amma ba sa samar da kuzari sosai ga kuma karancin sinadarai masu gina jiki. Saboda suna dauke da sinadaran dake yakar abinci mai gina jiki wadanda ke toshe hanyoyin da wasu muhimman sinadarai ke shiga cikin jiki.

Maiyo ta kara da cewa, idan aka markada hatsin da sinadaran da aka tattara daga gyaren da amaranth, za a samu kunun filawa mai cikakken dandano daidai da ninki biyu na sinadarin furotin, da ninki biyu zuwa uku na danyen kitse, da ninki biyu na sinadaran iron da zinc.

Kusan dukkan al’ummar nahiyar Afirka, kama daga yara har zuwa tsoffi, suna shan nau’in kunun na Afirka ko dai mai kauri ko ruwa-ruwa. Haka kuma abinci ne da ake amfani da shi wajen yaye jarirai, kana abinci mai gina jiki ga mata masu shayarwa, tsofaffi da wadanda ke murmurewa daga jinya, da karin kumallo, da nishadi, yayin da wasu ke shan sa a matsayin abinci.

Masani a cibiyar nazarin kwari da muhalli ta kasa da kasa (ICIPE) Chrysantus Mbi Tanga, ya ce kunun gyare mai kauri ya dara ka’idojin sinadaran abinci masu gina jiki da ake hadawa daga hatsi, inda sinadarin furotin da ke cikinsa ya kai tsakanin giram 15-16 a cikin kowane giram 100, kana sinadarin dake kara kuzari ya kai kilo 408-414 na sinadarin calories a cikin kowane gram 100.

Rashin abinci mai gina jiki, babbar matsalar kiwon lafiya ce da ake fama da ita a galibin kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka da ma wasu kasashen da suka ci gaba musamman tsakanin yara da mata. Rashin abinci mai gina jiki, yana haifar da tsunburewa, kasala da rashin kiba a yara.

Babban darekta kuma babban jami’in zartarwar cibiyar ICIPE, Segenet Kelemu ya bayyana cewa, Allah ya albarkaci nahiyar Afirka, da sauran yankuna masu tasowa da tarin dabbobi da tsirrai, sai dai ba a cin gajiyar yawancinsu. (Ibrahim Yaya)