logo

HAUSA

Ministan wajen Mali: Sin ta shiga kyakkyawan tafarkin raya hakkin dan Adam

2022-06-21 19:06:37 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar 'yancin rayuwa da samun ci gaba a matsayin muhimman hakkokin dan-Adama, kana tana bisa tafarkin da ya dace wajen raya hakkin dan-Adam cikin nasara, wannan shi ne abin da kasashen yankin Sahel ya dace su yi koyi da shi.

Diop ya bayyana haka ne a yayin bude taron karawa juna sani game da “yancin rayuwa da ci gaba su ne muhimman abubuwa game da raya hakkin dan-Adam a kasashen yankin Sahel" da aka gudanar a wannan rana. (Ibrahim)