logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya ya halarci bikin "ranar dafa abinci" na shekarar 2022

2022-06-21 20:15:36 CMG Hausa

A ranar 18 ga watan Yunin wannan shekara ce, cibiyar kula da baki da yawon bude ido ta Najeriya, ta shirya bikin "ranar dafa abinci mai dorewa ta kasa da kasa" a babban dakin taro dake Abuja, babban birnin Najeriya.

An gayyaci jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun don halartar bikin tare da gabatar da al'adun kasar Sin. Jakada Cui ya bayyana cewa, yana fatan kasashen Sin da Najeriya, za su hada gwiwa don cimma moriyar juna a nan gaba. (Ibrahim)