logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Nasarorin Sin a yaki da fatara abin koyi ne ga kasashe masu tasowa

2022-06-21 10:21:51 CMG Hausa

Wani kwararren masani a Najeriya ya ce, nasarorin da kasar Sin ta cimma a yaki da fatara ta samar da wani muhimmin darasi da ya kamata kasashe maso tasowa su koya domin tsame dunbun al’ummunsu daga cikin yanayin kangin talauci a cikin kayyedadden lokaci.

A wata hirar da ya yi kwanan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, babban birnin Najeriya, dakta Sheriff Ghali Ibrahim, shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa na jami’ar Abuja, ya ce kasar Sin, a kokarinta na tsame sama da mutane miliyan 800 daga kangin fatara a cikin kasa da shekaru takwas, ta yi amfani da dabaru na zahiri, kuma ta gwadawa duniya cewa ita jagora ce. Don haka, ya kamata kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, da na Latin Amurka, da na Caribbean, su yi koyi da kasar Sin a shirinta na yaki da fatara.

A tsokacin da masanin ya yi ya ce, hangen nesan da kasar Sin ta yi, ya taka muhimmiyar rawa a shirinta na yaki da talauci, inda ya bukaci kasashe masu tasowa dake da dunbun albarkatun kasa, da su yi amfani da su wajen tsara dabarun yadda za su tinkari yaki da fatara a kasashensu. (Ahmad)