logo

HAUSA

Abdulmalik Isma’il: Na koyi abubuwa sosai a lokacin da nake aiki tare da mutanen China

2022-06-21 15:26:44 CMG Hausa

Abdulmalik Isma’il, dan asalin Maidugurin jihar Borno ne dake arewa maso gabashin Najeriya, wanda ya yi shekaru sama da 15 yana aiki tare da wani kamfanin gine-gine na kasar Sin da ake kira CGC a Najeriya.

A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Abdulmalik ya bayyana yadda yake jin dadin aiki da mu’amala tare da mutanen China, da yadda ya fahimci halayen mutanen kasar. Ya kuma ce, rashin zama da su ya sa wasu mutane ke yiwa mutanen China mummunan fahimta.

Malam Abdulmalik yana kuma fatan koyawa sauran mutanen Najeriya fasahohin aiki da ya koya daga wajen mutanen China. (Murtala Zhang)