logo

HAUSA

Shugaban Afrika ta kudu yace hadin gwiwa da BRICS zai taimakawa kasarsa farfadowa daga annobar COVID-19

2022-06-21 10:54:06 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce kasarsa za ta samu alfanu masu yawa daga hadin gwiwarta da kungiyar kasashen BRICS, a yayin da kasar ke kokarin gudanar da ayyukan sake gina kasa daga mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar, shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatarwa ’yan kasar na mako-mako a ranar Litinin.

Ya ce martabar kasar Afrika ta kudu a matsayin mamban kasashen BRICS yana cigaba da karuwa, tun bayan da kasar ta shiga kungiyar yau shekaru 12 da suka gabata, inda ya bayyana hakan gabanin taron kolin BRICS karo na 14 da za a gudanar a ranar Alhamis.

Ramaphosa ya ce, huldar cinikayya tsakanin kasar Afrika ta kudu da sauran kasashe hudu na BRICS, ya kai dala biliyan 43.8 a shekarar 2021, inda ya zarta dala biliyan 30.4 na shekarar 2017.

A cewar shugaban, taron kolin wani muhimmin dandali ne ga kasar Afrika ta kudu, inda za ta karfafa dangantakarta da kasashe abokan huldarta, domin samun taimako don bunkasa ci gaban kasar, da samar da guraben ayyukan yi, kuma zai kasance a matsayin wata dama ce ga Afrika ta kudu, wajen bayar da gudunmawarta ga ci gaban duniya, yayin da ake fatan dukkan kasashen duniya za su samu kyakkyawar damar farfadowa daga mummunan tasirin annobar COVID-19. (Ahmad)