logo

HAUSA

Ya Kamata Kasashen Yamma Su Yi Hangen Nesa Game Da Tasirin Rikicin Ukraine Kan Kasashe Masu Tasowa

2022-06-20 17:28:49 CMG Hausa

Tuni farashin kayayyakin amfanin gona ya yi tashin gwauron zabi a sassan duniya daban daban, sakamakon rikicin Rasha da Ukraine, wanda a yanzu ya zarce watanni uku da barkewa. Alkaluman shirin samar da abinci na MDD sun tabbatar da cewa, duniya ba ta taba ganin kalubalen tsadar cimaka sama da na wannan lokaci ba, tun bayan yakin duniya na biyu, lamarin da kuma ke zuwa a gabar da duniya ke fuskantar tasirin annobar COVID-19, wadda ita ma ta haifar da komadar tattalin arzikin duniya.

Yayin da kasashen yammacin duniya ke ta kokarin dora alhakin hauhawar farashin kayayyakin amfanin gona ga kasar Rasha, su ma a nasu bangare sun taka rawar gani wajen ingiza girman wannan matsala.

Ga misali, shi kan shi rikicin Rasha da Ukraine, kasashe biyu masu fitar da tarin albarkatun gona ga sassa daban daban na duniya, ya samo asali ne sakamakon kokarin fadada ikon kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashin turai. Kuma duk da yunkuri da aka yi na hawa teburin shawara tsakanin Rasha da Ukraine, Amurka a nata bangare, ta yi ta kokarin rura wutar rikicin ta hanyar samarwa Ukraine makamai domin tunkarar Rasha, wanda hakan ke kara tsawaita mummunan tasirin tashin hankalin.

A zahiri, tsawaitar wannan tashin hankali zai ci gaba da ingiza  asarar da Rasha da Ukraine za su kirga, a hannu guda kuma, hakan zai haifar da kamfar abinci a sassa masu yawa na duniya, musamman kasashe masu tasowa, dake dogaro sosai kan cimakar da ake fitarwa daga kasashen biyu.

Ko shakka ba bu, yunkurin Amurka na kakaba takunkumin cinikayyar albarkatun gona da takin zamani da kasar Rasha ke fitarwa, ya haifar da hauhawar farashin cimaka da kaso sama da 30 bisa dari a kasashe masu tasowa. Irin wadannan kasashe masu tasowa, da sauran masu raunin tattalin arziki, na shan matsin lambar rayuwa, sakamakon manufofin takara, da kokarin tabbatar da iko na wasu kasashen yamma, wannan yanayi ne da bai dace ba, domin kuwa, kamata yayi manyan kasashen yamma masu karfin fada a ji, su taimaka wajen fitar da kasashe masu tasowa daga wahalhalu, maimakon aiwatar da matakai na kara jefa su cikin mawuyacin hali. (Saminu Alhassan)