logo

HAUSA

Habasha ta samu habakar kudaden shiga daga fitar da nama zuwa ketare

2022-06-20 13:35:18 CMG HAUSA

 

Kasar Habasha ta samu kudaden shigar da ya kai dala miliyan 110 daga hada-hadar fitar da nama zuwa ketare a watanni 11 na farkon kalandar gargajiya ta Habasha ta shekarar 2021/2022, wadda ta fara daga ranar 8 ga watan Yuli, kamar yadda wani jami’in kasar Habashan ya bayyana.

Jami’in dake lura da tsafta da ingancin wuraren sarrafa naman da ake fitarwa ketare a hukumar kula ayyukan gona ta kasar Habasha (EAA), Ayalew Shumet, ya bayyana cewa, kasar ta samu adadin kudaden ne ta hanyar fitar da nama zuwa ketare da ya kai ton 21,000 a cikin wannan wa’adi.

Shumet, ya kuma bada shawara cewa, akwai jan aiki dake gaban kasar ta gabashin Afrika game da yadda zata kara bunkasa kamfanonin fitar da nama zuwa ketare.

Jami’in hukumar ta EAA ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar nan gaba kasar Habasha za ta iya fitar da nama zuwa ketare da ya kai ton 300,000 a kowace shekara, sannnan za ta iya samun kudaden shigar da za su kai dala biliyan 1.5 daga fannin.

Sai dai kuma, domin cimma wannan hasashen, Shumet ya ce, ya kamata a inganta samar da dabbobi, da tsarin kiwon dabbobin, da kuma kasuwannin sayar da dabbobin. (Ahmad)