logo

HAUSA

Jakadan MDD: Janyewar dakarun MONUSCO daga lardin Tanganyika na Kongo DRC alamun ingantuwar tsaro ne

2022-06-20 11:04:53 CMG HAUSA

 

Bruno Lemarquis, mataimakin wakilin musamman na babban sakataren MDD a demokaraiyyar Kongo DRC ya bayyana cewa, janyewa dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a Kongo DRC (MONUSCO) daga gabashin lardin Tanganyika, wani labari ne mai dadin ji dake nuna cewa yanayin tsaro ya inganta a shiyyar.

Wasu bayanai da aka fitar ranar Lahadi sun nuna cewa, Lemarquis yana ziyarar aiki a lardin Tanganyika tun daga ranar 17 ga watan Yuni, a shirye-shiryen da ake na kwashe dakarun MONUSCO daga Tanganyika.

Ya ce yana da muhimmanci a fayyacewa al’umma cewa, janyewa dakarun MONUSCO, hakan ya dace ne bisa la’akari da ingantuwar yanayin tsaro a lardin, sai dai hakan ba ya nufin ficewar MDD ba ne. Ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci shi ne mutane sun riga sun fahimci hakan, sannan ya yi alkawarin cewa sauran bangarori na MDD za su ci gaba da zamansu a lardin nan Tanganyika.

A wata sanarwa da aka baiwa manema labarai, adadin dakarun wanzar da zaman lafiya na MONUSCO dake zaune a yankin, da suka hada da kwararru, za su ci gaba da zama a yankin nan da wasu watanni masu zuwa domin a samu nasarar janyewa dakarun na MONUSCO lami lafiya. (Ahmad)