logo

HAUSA

Batun mika 'yan gudun hijira ya nuna halayyar kasashen yamma

2022-06-20 17:08:51 CMG Hausa

'Yan gudun hijira mutane ne mafi fama da mawuyacin hali a duniya. Idan dai akwai dama, to, ba za su yi watsi da gidajensu, da barin iyalai, har su fita zuwa wata kasa ta daban ba, inda suke jure zaman rayuwa cike da wahalhalu. Sai dai yanzu har ana kara wulakanta su: Kasar da suke kaura cikinta ka iya tusa keyarsu zuwa wani wuri mai nisa, inda ba su taba tunani ko tsammanin zuwa ba.

A ranar 14 ga wata, kotun kare hakkin dan Adam ta nahiyar Turai ta hana tashin wani jirgin sama mai daukar nauyin jigilar ‘yan gudun hijira daga kasar Birtaniya zuwa Rwanda. Kafin afkuwar lamarin, kasar Birtaniya da Rwanda sun kulla wata yarjejeniya, inda aka daddale cewa, Birtaniya zata biya kudi fam miliyan 120 ga Rwanda, don kasar Rwandan ta karbi ‘yan gudun hijira da suka yi satar ketarawa zuwa kasar Birtaniya. Ko da yake, ba a fara gudanar da yarjejeniyar ba tukuna, sakamakon kin amincewar da bangarorin kasa da kasa suka nuna, ciki har da hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD suka nuna. Amma gwamnatin kasar Birtaniya tana ci gaba da neman aiwatar da yarjejeniyar.

Me ya sa ake kin amincewa da matakin da kasar Birtaniya ta dauka?

Saboda da farko dai, kasar Birtaniya, da Amurka, da sauran kasashen yammacin duniya, laifinsu ne yadda suka haddasa matsalar samun tarin ‘yan gudun hijira a duniya. Wadannan kasashe sun kaddamar da yake-yake a kasashen Iraki, da Afghanistan, da tsoma baki tare da tsananta yanayin rikici a Syria, da Libya, da Venezuela, da dai sauransu. Irin matakan da suka dauka sune ainihin dalilan da suka haddasa karuwar ‘yan gudun hijira a duniya. Saboda haka ya kamata kasashen yamma su dauki nauyin kula da ‘yan gudun hijira, maimakon a tusa keyarsu zuwa wata kasar dake nahiyar Afirka.

Ban da wannan kuma, matakin kasar Birtaniya ya nuna wani yanayi na rashin adalci, inda matukar akwai kudi, to, ana iya yin kome. Su kasashe masu sukuni, sai su biya kudi, sa’an nan za su iya magance daukar nauyin kulawa da ‘yan gudun hijira. Ganin haka zai sa su ta da rikici, da lalata yanayin zaman rayuwar jama’ar sauran kasashe, ba tare da wata damuwa ba. Idan an samu ‘yan gudun hijira, sai a tusa keyarsu zuwa kasashe masu tasowa, ba tare da tsoron samun wani tasiri daga lamarin ba.

Sa’an nan lamarin ya nuna halayyar kasashen yamma a fannin hakkin dan Adam. Da ma kasashen suna kallon kansu a matsayin “Masu kare hakkin dan Adam a duniya”, har ma su kan tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe. Sai dai ko da gaske ne suna kare hakkin dan Adam a duniya? Idan mun dauki kasashen Amurka da Birtaniya a matsayin misali. Kasar Amurka ta yi ta kaddamar da yake-yake a kasashe da dama, inda take kisan mutanen kasashen, da aiwatar da mulkin danniya a duniya. Yayin da a nata bangare, kasar Birtaniya tana kallon ‘yan gudun hijira a matsayin kayayyaki, tana neman mika su ga sauran kasashe ba tare da kulawa da yanayin da wadannan mutane suke ciki ba. Ta wadannan batutuwa, za mu iya ganin cewa, kasashen yamma kullum suna neman sanya sauran kasashe kulawa da hakkin dan Adam, maimakon su da kansu su yi haka.

Batun nan ya shaida gaskiyar wata tsohuwar magana dake cewa: “A yi bincike kan halayyar wani mutum bisa aikace-aikacensa, maimakon kalmomin da ya fada”. (Bello Wang)