logo

HAUSA

Adadin mutanen da zazzabin Lassa ta kashe a Najeriya ya kai 155

2022-06-19 16:54:23 CMG Hausa

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC ta sanar cewa, yawan mutanen da cutar zazzabin Lassa ta kashe a cikin wannan shekara a kasar ya karu zuwa 155, a yayin da gwamnatoci ke daukar matakan dakile bazuwar cutar a fadin kasar.

A rahotannin baya bayan nan game da cutar zazzabin Lassa da suka iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Asabar, sun nuna cewa, hukumar dakile cutukan ta bayyana cewa, an samu adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kimanin 782, yayin da adadin wadanda ake zaton sun kamu da cutar ya kai 4,939, tun daga farkon wannan shekara.

Yayin da aka samu adadin wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar 155 ya zuwa farkon watan Yuni, hukumar NCDC tace, adadin hasarar rayukan da aka samu a kasar ya kai kashi 19.8 bisa 100, wanda ya ragu idan an kwatanta da kashi 20.2 bisa 100 da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2021. Kuma jahohi 24 na kasar sun bada rahoton kamuwa da cutar na akalla mutum guda a wannan shekarar, yayin da jihohi uku na Ondo, da Edo da jahar Bauchi, su ne ke da kashi 68 bisa 100 na yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, zazzabin Lassa, wata cuta ce mai tsanani wadda kwayoyin cutar Lassa ke haddasawa, kuma tana daga cikin rukunin dangin kwayoyin cutar arenavirus. Mutane suna iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa ne ta hanyoyin abinci ko kayan amfanin gida wadanda fitsari ko wani abu mai damshi daga jikin beraye nau’in Mastomys ya taba. Ana samun yawaitar kamuwa da cutar ne daga jikin beraye a yankunan kasashen yammacin Afrika.(Ahmad)