logo

HAUSA

An yi zanga-zanga a Landan don nuna adawa ga hauhawar farashin kaya

2022-06-19 16:10:01 CMG Hausa

Jiya ranar 18 ga wata, a kasar Birtaniya, an yi zanga-zanga a birnin Landan, fadar mulkin kasar, domin nuna adawa game da hauhawar farashin kayayyakin yau da kullum, dubban masu zanga-zanga sun yi ta kiraye-kiraye ga gwamnatin kasar, inda suka bukaci ta fitar da karin manufofin daidaita matsalar raguwar darajar kudi.

An lura cewa, darajar kudin Birtaniya tana raguwa a kai a kai, sakamakon tasirin da rikici tsakanin Rasha da Ukraine da takunkumin da aka kakkabawa Rasha suke kawowa ga fannin samar da makamashi da abinci, har kudin da al’ummun Birtaniya ke kashewa a rayuwar yau da kullum ya karu bisa babban mataki, kuma gwamnatin kasar ba ta dauki matakan da suka dace kan matsalar ba, don haka ta gamu da suka da zargi daga al’ummun kasar.

Babban bankin Birtaniya ya bayyana a ranar 16 ga wata cewa, an yi hasashen cewa, GDPn kasar a rubu’in biyu wato daga watan Aflilu zuwa Yuni zai ragu da kaso 0.3 bisa dari, kuma ma’aunin CPI zai kai sama da kaso 9 a cikin watanni masu zuwa, har zai zarta kaso 11 bisa dari a watan Oktoba.

Sakamakon binciken ra’ayin jama’a da aka samu ya nuna cewa, sama da rabin iyalai a kasar Birtaniya sun gamu da matsalar rayuwa, yanzu haka al’ummun kasar sun fi son sayen kayayyakin da aka rage farashinsu, kuma sun rage yawan kifi da nama da albasa da suke saya domin tsimin kudin kashewa, har wasu sun daina tuka mota domin tsimin mai. (Jamila)