logo

HAUSA

Ministan cinikin Afrika ta Kudu yayi maraba da kawar da shinge ga amfani da fasahar samar da riga-kafin COVID-19

2022-06-19 16:03:58 CMG Hausa

Ministan ciniki da harkokin masana’antu na kasar Afrika ta Kudu, Ebrahim Patel, yayi maraba da yarjejeniyar da kungiyar kasuwanci ta duniya WTO ta cimma, game da janye shinge na amfani da fasahohi don samar da riga-kafin annobar COVID-19, watanni 20 tun bayan da kasar Afrikan ta gabatar da bukatar neman kawar da shingen domin samun nasarar yaki da annobar.

A yayin taron ministocin WTO karo na 12, wanda aka kammala a ranar Juma’a a helkwatar kungiyar WTO dake birnin Geneva, na kasar Switzerland, mambobin kasashen kungiyar sun cimma matsaya kan muhimman batutuwa, kamar batun yaki da annobar, da batutwan dake shafar janye shinge na hakkin mallakar fasaha wato TRIPS, don tinkarar batutuwan dake da nasaba da yaki da annobar COVID-19.

Yarjejeniyar ta baya bayan nan, ta bada dama ga gwamnatoci dasu ba masana’antun cikin gida izinin samar da riga-kafin, ko kuma sinadaran hada riga-kafin, kana an bada izinin yin amfani da fasahohin samar da riga-kafin ba tare da neman mallakar fasahohin ba har na tsawon shekaru biyar.(Ahmad)