logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya kaddamar da aikin gyara wurin hakar sinadarin Lithium da kamfanin Sin zai aiwatar

2022-06-18 17:16:35 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya halarci bikin kaddamar da aikin gyara wurin hakar sinadarin Lithium na Bikita, wanda shi ne irinsa mafi girma a kasar.

Kamfanin Sinomine Resource Group na kasar Sin ne ya sayi wurin na Bikita a watan Janairun bana, inda yake shirin zuba jarin dalar Amurka miliyan 200 don gyaran sa, da nufin inganta aikin samar da sinadarin Lithium da kara samar da aikin yi a yankin.

Shugaba Mnangagwa ya bayyana a gun bikin cewa, gwamnatin kasar Zimbabwe na ba da muhimmanci ga kamfanonin Sin da suka zuba jari a kasar. Ya ce a shekarun baya-baya nan, kamfanonin Sin da dama sun zuba jari a kasar a fannonin ayyukan more rayuwa da hakar ma’adinai da aikin noma da sadarwa da sauransu, wadanda suke amfanawa masu zuba jarin da kuma yankunan dake samun jarin.

Shugaba Mnangagwa ya kara da cewa, yana fatan za a yi amfani da jarin waje ciki har da jarin Sin, don sa kaimi ga kasar Zimbabwe wajen hakar sinadarin Lithium yadda ya kamata, da taimakawa kasar wajen cimma burin samun kudi dalar Amurka biliyan 12 daga bangaren hakar ma’adinai a shekarar 2023. Kana yana fatan masu zuba jari za su taimakawa kasar Zimbabwe wajen inganta karfin kera kayayyaki da bunkasa masana’antu don kara samar da gudummawa wajen samar da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba. (Zainab)