logo

HAUSA

An gudanar da jana’izar mutanen da suka mutu a harin wata mujami’a a Nijeriya

2022-06-18 16:13:17 CMG Hausa

Hukumomi a Nijeriya, sun gudanar da jana’izar mutanen da suka mutu sanadiyyar harin da aka kai wata mujami’a a jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar.

A jawabin da ya gabatar kafin jana’izar a jiya, gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu, ya ce jimilar gawarwaki 22 ne aka shirya binnewa jiyan a garin Owo na Ondo, inda harin ya auku, a ranar 5 ga wata, a mujami’ar Katolika ta St. Francis.

A cewar gwamnan, jimilar mutane 40 ne suka mutu yayin harin, inda akalla wasu 61 suka jikkata, yana mai cewa, iyalan mamata 18 da suka gaza jiran shirin hukumomi na gudanar da jana’izar na bai daya, sun riga sun binne ‘yan uwansu.

A makon da ya gabata ne, gwamnatin Nijeriya ta dora alhakin harin kan kungiyar ISWAP ta masu tsattsauran ra’ayi.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Rauf Aregbesola, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an umarci hukumomin tsaro su farauto maharan tare da gurfanar da su, yana mai nanata cewa, harin ba shi da wata alaka da kabilanci ko addini, inda ya jadadda cewa, ayyukan kungiyar ISWAP ba su yi daidai da koyawar wani addini ba. (Fa’iza Mustapha)