logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya yi kira da a kara daukar matakan magance lalacewar gonaki

2022-06-18 17:23:26 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi jawabi albarkacin ranar yaki da kwararowar hamada da bala’in fari ta duniya dake gudana a duk ranar 17 ga watan Yuni, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su kara daukar matakai don magance lalacewar gonaki a duniya.

Guterres ya bayyana cewa, kimanin rabin yawan mutanen duniya sun fuskanci matsalar lalacewar gonaki. Kuma a kusan dukkan yankunan duniya, an kara samun bala’in fari.

Ya ce sakamakon guguwar rairayi da kura, da gobarar daji da rashin samun girbi, da rashin matsuguni da karuwar rikice-rikice, mutanen duniya fiye da miliyan 100 sun shiga mawuyacin hali.

Guterres ya yi nuni da cewa, bala’in fari yana da nasaba da sauyin yanayi, kana yana da nasaba da hanyoyin sarrafa kasa da dan Adam ke amfani da su. Don haka, tilas ne bil Adama su yi kokarin magance lalacewar gonaki.

Ya ce, zuba jari ga gonakin da aka farfado da su bayan sun lalace tare da amfani da su, zai samar da moriyar da ta ninka ta baya fiye da sau 10. Alal misali, shirin Great Green Wall na nahiyar Afirka ya taimaka wajen farfado da gonaki fiye da kadada miliyan daya, kana ya samar da dubban guraben aikin yi ga kasashen Afirka da dama. Ya ce duk da cewa akwai wannan kyakkyawan misali, ana bukatar kara daukar matakai a wannan fanni. (Zainab)