logo

HAUSA

Shirin Bidiyo Da Ya Nuna Yadda Sin Ta Fatattaki Talauci Ya Karfafawa ‘Yan Nijeriya Gwiwa

2022-06-18 16:35:54 CMG Hausa

Gomman mutane daga dukkan bangarorin rayuwa ne suka samu damar kallon yadda kasar Sin ta yi nasarar fatattakar talauci, a lokacin da aka nuna wani shirin bidiyo na documentary, wanda ya gabatar da baki dayan aikin yakar talaucin a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Bayan kammala kallon shirin, mutanen sun bayyana cewa, ya karfafa musu gwiwa, inda suka yi kira da a aiwatar da aikin yaki da talauci a Nijeriya.

Gidan talabijin na kasar Sin CGTN tare da hadin gwiwar gidauniyar Kuhn ta Amurka ne suka gabatar da shirin mai taken “Voices From The Frontline: China's War On Poverty,” wanda ya bayyana yadda kasar Sin ta fatattaki talauci, ta hanyar gabatar da misalan da suka nuna irin dabarun da kasar ta yi amfani da su.

Kallon wannan shirin da jama’a suka yi a Abuja, ya bude wata kofa ta bikin nuna shirye-shiryen bidiyo na kasar Sin a kasar mafi yawan al’umma a Afrika.

Bikin nuna shirye-shiryen dake da nufin yayata musayar al’adu tsakanin Sin da sauran kasashe dake fadin duniya, yayin da yake gabatar da al’adun kasar Sin da al’ummarta, zai fara ne da wani katafaren biki a Beijing, nan gaba cikin wannan wata, inda zai gudana har karshen shekara.

Yayin wa’adin bikin, wasu zababbun tashoshin talabijin za su nuna sama da shirye-shiryen bidiyo 50 da gidan talabijin na CGTN ya shirya, ciki har da wadanda suka samu lambar yabo kamar wancan da aka nuna a birnin Abujan Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)