Jawabin Xi Jinping Ya Kara Azama Kan Aiwatar Da Shawarar Bunkasa Duniya
2022-06-18 20:36:28 CMG Hausa
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarta tare da gabatar da jawabi ga taron tattalin arzikin duniya karo na 25 da aka yi a St. Petersburg. Dangane da jawabinsa, Tarek Elsonoty, mataimakin babban editan jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ya ce, shawarar bunkasa duniya da Shugaba Xi Jinping ya gabatar cikin jawabinsa ya fito da dabarar daidaita rikicin da ake fuskanta a duniya yanzu. Jawabin Xi ya nuna yadda kasar Sin take tsayawa tsayin daka kan manufar cudanyar sassa daban daban da kara azama kan cimma muradun bil Adama baki daya.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne a kara azama kan aiwatar da shawarar bunkasa duniya yadda ya kamata, a kokarin rayawa da kuma samun kyakkyawar makoma mai zaman lafiya da wadata. Shugaban na kasar Sin ya kuma gabatar da shawara a fannoni 4, wato da farko, akwai bukatar samar da kyakkyawan yanayin neman ci gaba. Na biyu, ya kamata a karfafa hadin gwiwa a fannin neman ci gaba. Na uku, a inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya, sai na hudu, a ingiza neman ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire.
Shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar bunkasa duniya a babbar muhawara ta babban taron MDD karo na 76 a watan Satumban shekarar 2021, shawarar da ta biya bukatun kasa da kasa na gaggauta samun farfadowa. MDD da kasashe fiye da 100 sun goyi bayan shawarar, wadda za ta gaggauta aiwatar da ajandar MDD dangane da raya kasa mai dorewa a shekarar 2030.
Cikin shekara guda da ta gabata, kasar Sin na kokarin tuntubar kasa da kasa, a kokarin ganin sabon ci gabanta ya samarwa da kasa da kasa sabuwar dama. Ana hasashen cewa, sakamakon aiwatar da shawarar, ya sa kasashen duniya sun kara cin gajiya cikin adalci. kasar Sin za ta cika alkawarinta na ganin ba a bar kowa a baya ba wajen samun ci gaba. (Tasallah Yuan)