logo

HAUSA

Shui Qingxia:Ba za mu yi watsi da burinmu na cimma nasara ba (A)

2022-06-17 15:40:36 CRI

Ita ce Shui Qingxia, mai horar da 'yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin, tun bayan kama kujerar take daukar nauyi da kalubale na jagorantar kungiyar fita daga mawuyacin hali. Tana kokari tare da kungiyarta don mika wata takardar amsa ta cimma gasar ta kofin Asiya ga al’ummar kasar baki daya. Da taushin hali da jajircewarta, ta canza makomar kungiyarta, da makomar gungun ‘yan mata, har ma da nata makoma. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da wannan baiwar Allah mai suna Shui Qingxia.

A shekarar 1983, Shui Qingxia mai shekarun haihuwa 17 a duniya ta  samu horo kan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Makarantar Wasannin Matasa ta yankin Hongkou na birnin Shanghai. Ta yi ta haka har tsawon shekaru 6, kuma ta zama zakaran pentathlon na daliban makarantar sakandare ta Shanghai. A wancan lokacin, tana fatan samun damar haskawa a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, amma an gaya mata cewa saboda tsayin da take da shi, idan ta ci gaba da yin wasan, to ba za ta samu sakamako mafi kyau ba.

Amma, abin farin ciki shi ne, kocin makarantar wasannin yana ganin cewa, Shui Qingxia na da hazaka, kuma abin takaici ne idan aka yi watsi da ita, a daidai wannan lokaci, an kafa kungiyar kwallon kafa ta mata a Shanghai, don haka kocin ya ba da shawarar shiga da Shui Qingxia kungiyar.

Lokacin da ta sami labarin cewa, za ta yi wasan kwallon kafa, Shui Qingxia ta yi mamaki sosai, ta ce, "Me ya sa aka bar ni in buga kwallon kafa? 'Yan mata suna buga kwallon kafa, yana da 'ban tsoro'!”

Irin abun da take ji ba abin mamaki ba ne. A wancan lokacin, wasan kwallon kafa na mata ya kasance sabon abu a birnin Shanghai har ma da kasar Sin baki daya, don haka yawancin Sinawa ba su fahimceshi sosai ba.

A wancan lokacin, Shui Qingxia ba ta tsammanin cewa, wasan kwallon kafa, wanda ya sa ta dan jinkirta, zai zama "babban jigo" da ba za ta iya yin kasa a gwiwa ba a rayuwarta ta nan gaba. A lokacin, tunaninta ya kasance mai sauki qwarai, "Tun da ana son in buga kwallon kafa, to bari in buga."

Don haka, Shui Qingxia ta fara wasan kwallon kafa a hukumance.

Lokacin da ta fara wasan kwallon kafa, Shui Qingxia ba ta san yadda za ta kare kanta ba, kuma ta kan ji rauni. Ko da yake wasan kwallon kafa yana da wahala, amma Shui Qingxia ta yi mamakin ganin cewa, tana da hazaka a wannan wasan. Tare da hazaka da kuma kokarin da take yi, Shui Qingxia ta yi sauri ta fice daga ‘yan matan kungiyar sama da 100, kuma ta shiga tawagar farko ta kungiyar kwallon kafa ta mata ta Shanghai a shekarar 1984. Kana, a shekarar 1986, an zabe ta shiga kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin.

Shui Qingxia ta kasance mai nazarin wasan kwallon kafa a ko da yaushe, a lokacin hutu, ta kan shafe yawacin lokutanta wajen kallon wasan, za ta rika lura da motsi, da dabarun 'yan wasa, da hadin gwiwar dake tsakanin shahararru 'yan wasa, da kuma kwarewarsu ta yin nazari wasan a fili, don ganin abin da za ta iya amfani da shi.

Bayan kallon manyan wasannin kwallon kafa na duniya, Shui Qingxia ta fara fahimtar nata kurakurai, tana bullo da wani tunani, wato samun horo a kasashen waje da sanin al'adun kwallon kafarsu. A shekarar 1992, Shui Qingxia, wadda ta shafe shekaru 9 tana buga kwallon kafa, ta shiga kungiyar kwallon kafa ta Prema ta kasar Japan, kuma ta kasance daya daga cikin 'yan wasan kwallon kafa mata na farko a kasar Sin da suka yi wasa a kasashen waje, tana da shekaru 26 kacal a wannan shekarar.

A kungiyar kwallon kafa ta Prima da ke kasar Japan, Shui Qingxia ta yi saurin zama jigo a kungiyar. Amma a shekara ta biyu da take a kasar Japan, Shui Qingxia ta ji rauni a wasan koyarwa da kungiyar wasan kwallon kafa ta maza, kuma aka saka farantin karfe mai tsayin centimita 30 a cikin kafarta ta dama.

Bayan ta ji raunin, Shui Qingxia ta dawo kasar Sin, kuma bayan watanni 5 kacal, ta bulla a filin atisaye na kungiyar kwallon kafa ta mata ta Shanghai.

Bayan ta murmure daga raunin da ta samu, Shui Qingxia, wadda ta shagaltu da horo da gasa, ba ta da lokacin damuwa da aikin tiyata, hakan wannan farantin karfe ya zauna a kafarta ta dama har tsawon shekaru 7.

A cikin fiye da shekaru goma na buga wasan kwallon kafa, Shui Qingxia ba ta taba tsayawa saboda jin rauni babba ko karami ba, muddin tana tafiya a filin wasa, ta kan manta  mene ne wahalla da gajiya, tana ta guje-guje kamar ba ta jin zafin raunin da take jikinta. Kocin yana damuwa da ita kuma sau da yawa ya yi mata tsawa a wajen filin: "Ki rage gudu kuma ki huta kadan."

A shekarar 1994, Shui Qingxia ta koma cikin kungiyar kasar Sin, kuma ta halarci gasar wasannin Asiya karo na 12 da aka yi a birnin Hiroshima na kasar Japan a wannan shekarar, inda ta jagoranci kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin wajen lashe lambar zinare.

A cikin gasar cin kofin Asiya guda biyu da suka biyo baya, Shui Qingxia ta taimaka wa kungiyarta lashe gasar. A shekarar 1997, ta kuma lashe gasar cin kofin Asiya karo na biyar a sana’arta.

Ya zuwa yanzu, kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta lashe gasar sau shida a jere tun bayan da ta halarci gasar cin kofin nahiyar Asiya a shekarar 1986, inda ta zama babbar kungiyar kwallon kafa ta mata ta farko a nahiyar. An kuma yi wa Shui Qingxia da abokan wasanta lakabin "'yan wasan zinare na kasar Sin".

A shekara ta 2001, Shui Qingxia 'yar shekaru 35 ta yanke shawarar "rataye takalmanta". Har ila yau, ba ta da shirin barin wasan kwallon kafa, ta riga ta tsara makomarta: wato za ta zama koci, irin tunanin da ta yi tun lokacin da take matashiya.