logo

HAUSA

Ya kamata a sanya binciken kare hakkin dan adam a Amurka cikin ajanda

2022-06-17 14:11:19 CMG Hausa

Yayin gudanar da taron kolin kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 50 wanda aka gudanar kwanakin kadan da suka gabata a Geneva, kasar Cuba ta fidda sanarwa a madadin kasashe kusan 70, inda ta nuna adawa da yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun hakkin dan adam. Bugu da kari, sama da karin kasashe 20 ne suka yi jawaban nuna goyon baya ga kasar Sin.

Kusan kasashe 100 ne suka yi jawabai game da kasar Sin ta hanyoyi daban-daban, inda hakan ke nuna cewa, al’ummar kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, sun fahimci makirci da yin baki biyu da Amurka da wasu kasashen yammacin duniya ke yi kan batutuwan dake shafar hakkin dan adam, kuma sun bayyana cikakkiyar matsayarsu na yin adawa da Amurka da kasashen yamma, inda suke amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin makaman siyasa wajen kai hari kan abokan adawarsu.

A hakikanin gaskiya, kowa ya sani cewa idan ana magana kan batun take hakkin dan Adam, kasar Amurka ta kasance a matsayin kanwa uwar gami. Yayin da kasar Amurka ke kalubalantar sauran kasashe kan batun hakkin dan adam, ya kamata kasashen duniya su kalli batun a mahanga mafi girma. Batun binciken kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD kan yanayin take hakkin dan Adam a Amurka, ya kamata a sanya shi cikin ajanda ba tare da bata lokaci ba.(Ahmad)