logo

HAUSA

Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar hamayya ya zabi mataimaki

2022-06-17 10:26:12 CMG Hausa

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP, ta tabbatar da Ifeanyi Okowa, gwamna mai ci na jahar Delta mai arzikin mai, a matsayin mataimakin dan takarar neman shugabancin kasar Atiku Abubakar, a babban zaben kasar na shekara mai zuwa.

Okowa, mai shekaru 62, kana gwamnan jahar Delta a wa'adin mulki na biyu, ya amince da zabin da Atiku Abubakar yayi masa a matsayin wanda zai yi aiki tare da shi domin kalubalantar jam'iyyar APC mai mulkin kasar a zabe mai zuwa.(Ahmad)