logo

HAUSA

Harin BH ya yi sanadin rayuka 6 a Kamaru

2022-06-17 10:06:44 CMG Hausa

Fararen hula akalla 6 ne suka mutu yayin wasu hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai yankin arewa mai nisa na Kamaru.

Mayakan sun kai harin ne wasu kauyuka biyu na garin Darak dake yankin, da misalin karfe 8 na dare a ranar Laraba, inda suka kuma kone gidaje 30 tare da barin mazauna cikin halin ni ‘yasu.

Wata majiya daga rundunar sojin kasar ta sanarwa Xinhua cewa, an yi jana’izar mamatan da safiyar jiya Alhamis.

Ta kara da cewa, rundunar na matsa kaimi wajen daukar matakan tsaro a yankin, biyo bayan hare-haren da ake kai masa a kai a kai.

Rahotannin tsaro sun bayyana cewa, mayakan sun farwa garuruwa 5 dake yankin a cikin mako guda da ya gabata, inda suka kashe akalla mutane 5. (Fa’iza Mustapha)