logo

HAUSA

IMF: Tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da samun kuzari

2022-06-17 09:55:06 CMG Hausa

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da samun kuzari a bangarorin bayar da hidima da aikin gona, inda aka yi hasashen alkaluman GDP na kasar za su kai kaso 3.4 a bana.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua a jiya, asusun IMF ya ce alkaluma na baya bayan nan, sun nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun ci gaba a kusan dukkan bangarori, in ban da na man fetur dake ci gaba da fama da kalubalen tsaro da na fasahohi.

Rahotanni daga kafofin watsa labarai na kasar sun ce yawan man da kasar ke samarwa ya sauka da kaso 23.8, zuwa ganga miliyan 1.024 a kowacce rana, ya zuwa watan mayun bana, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.344 da take samarwa a makamancin lokacin a bara. (Fa’iza Mustapha)