logo

HAUSA

Sin za ta taimakawa Tanzania bunkasa ilimin sana’o’in hannu

2022-06-17 11:37:09 CMG Hausa

Kasashen Sin da Tanzania, sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwa dake da nufin bunkasa ilimin sana’o’in hannu, ta hanyar samar da sabon mizani a bangaren, a kasar ta gabashin Afrika.

shirin kawance kan ilimin sana’o’in hannu tsakanin Sin da Afrika ne ya dauki nauyin sabon shirin na nazari da inganta mizanin kwarewar aiki da aka kaddamar a ranar Laraba, inda zai gudana karkashin kulawar majalisar kula da ilimin fasahohi da sana’o’in hannu ta kasar Tanzania (NACVET).

A cewar Jiang Yilin, sakatare janar na shirin kawancen Sin da Afrika, jimilar kwalejojin koyar da sana’o’in hannu 43 na kasar Sin ne za su shiga kashin farko na shirin da ya kunshi mizanin sana’o’in hannu daban daban guda 54.

A nasa bangaren, babban sakataren NACVET Adolf Rutayuga, cewa ya yi, shirin zai saukaka raya ilimi da horon sanan’o’in hannu a Tanzania, haka kuma zai shimfida tubalin kafa sabon mizanin ilimi.

Ya kara da cewa, shirin zai kuma taimaka wajen samar da dimbin ma’aikata masu basira, da tabbatar da wadanda za a yaye a bangaren, sun cimma bukatun kasuwar duniya da daukaka matsayin masana’antun kasar. (Fa’iza Mustapha)