logo

HAUSA

Ya Kamata ‘Yan Siyasan Birtaniya Su Rika Yin Abu Gwargwadon Karfinsu

2022-06-16 20:49:16 CMG Hausa

Jiya Laraba hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai wato EU ta kai karar gwamnatin Birtaniya saboda rashin mutunta wasu tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar Arewacin Ireland. Madam Michelle O’Neil, mataimakiyar shugaban jam’iyyar Sinn Féin ta Arewacin Ireland, jam’iyyar da ke goyon bayan rabuwar Arewacin Ireland daga Birtaniya, ta nuna cewa, abun da gwamnatin Birtaniya ta yi ya kara tada kura a yanayin siyasar yankin Arewacin Ireland. Kwanaki 2 kafin wannan kuma, madam Nicola Sturgeon, babbar jami’in mahukuntan Scotland ta sanar da cewa, ko gwamnatin Birtaniya ta yarda ko a’a, za ta kara azama kan jefa kuri’a kan ficewar Scotland daga Birtaniya a shekara mai zuwa a Scotland.

Lallai abubuwan da Arewacin Ireland da Scotland suka yi sun kara damun gwamnatin Birtaniya, wadda ta dade tana fuskantar matsaloli da dama. Duk da haka, ‘yan siyasan Birtaniya suna tada zaune tsaye inda suke goyon bayan kasar Amurka, a yunkurin ta da rikici a Turai da nahiyar Asiya da tekun Fasifik. Abin da suke sha’awa shi ne ta da rikici a duniya. Abun da suke yi, ya sa kasashen duniya na yi musu dariya. (Tasallah Yuan)