logo

HAUSA

Batun Taiwan batu ne na cikin gidan kasar Sin

2022-06-15 08:20:34 CMG Hausa

A kwanakin baya ne mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan tsaron kasar Wei Fenghe, ya gabatar da jawabi kan ra'ayin kasar Sin, game da odar yankin a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 19 da aka gudanar a kasar Singapore.

Mahukuntan kasar Sin sun sha bayyana cewa, babu mai iya dakushe ci gaban kasar Sin, kuma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen neman ci gaba cikin lumana. Don haka, ci gaban kasar Sin ba barazana ba ce ga wasu. Sabanin haka, hakan wata babbar gudummawa ce ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. Ya ce kasar Sin tana nacewa kan manufar tsaron da ta dace da yanayin tsaro.

A game da batun yankin Taiwan kuwa, Wei ya ce Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, kuma batun Taiwan harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Kuma babu shakka, duk masu neman 'yancin kai na Taiwan a kokarin raba kasar Sin, hakika zai zo karshe, haka kuma tsoma bakin kasashen waje ba zai taba yin nasara ba.

Ya ci gaba da cewa, sake hadewar Taiwan da babban yanki cikin lumana, shi ne babban fatan al'ummar Sinawa. Wei ya ce, duk wanda ya kuskura ya nemi tayar da batun ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, hakika ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da duk wani martani da ya dace, kuma za mu mayar da martani ko ta halin kaka. Bai kamata wani ya raina karfin da sojojin kasar Sin suke da shi na kare iko da cikakkun yankunanta ba. Duk wadannan na zuwa ne, bayan da Amurka ta fito karara tana tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ba tare da hujjoji ba.

Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta dakatar da shafa mata kashin kaji, da neman dakile ci gaban ta, kana ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta. Amma idan Amurka tana son yin fito-na-fito da Sin, to, kasar Sin ba za ta ja da baya ba. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)