logo

HAUSA

An kashe gendarmomi 8 a wani hari a Nijer

2022-06-15 11:25:14 CMG Hausa

Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe jami’an tsaron gendarmomi 8, da kuma jikkata wasu 33, a harin ta’addanci da suka kaddamar a kusa da kan iyakar Nijer da Burkina Faso, gwamnatin Nijer ta sanar da hakan a ranar Talata.

A sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce, mayakan ‘yan ta’addan dauke da makamai kan babura da wasu motoci, sun kaddamar da hari kan dakarun tsaron a yankin Waraou dake shiyyar kudu maso yammacin jamhuriyar Nijer, da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Talata, a lokacin da dakarun gendarmomin ke gudanar da aikin sintiri don tabbatar da tsaro a wasu kauyuka dake kusa.

Sai dai ma’aikatar tsaron ta ce, kusan ‘yan ta’adda 50 aka kashe, yayin da gendarmomi shida daga cikin wadanda aka raunata, suna cikin yanayi mai tsanani.(Ahmad)