logo

HAUSA

Matasan Afrika na ganin kasar Sin a matsayin mai bayar da gagarumar gudunmuwa a nahiyar

2022-06-15 10:38:06 CMG Hausa

Rahoton gidauniyar Ichikowitz ta kasar Afrika ta kudu, ya nuna cewa, matasan Afrika na ganin kasar Sin a matsayin kasa mafi tasiri a nahiyar, inda take bayar da gudunmuwa wajen raya ababen more rayuwa da bayar da horo.

Rahoton nazari matasan Afrika na 2022, wanda aka gudanar a kasashen Afrika 19, aka kuma wallafa a ranar Litinin, ya nuna cewa, sama da rabin matasan nahiyar wato kaso 54, sun ce kasar Sin na yin gagarumin tasiri a kasashensu. Kusan daukacin matasan kasashe 3 ne suka amince cewa kasar Sin ce mafi tasiri a Afrika, kasashen sun hada da Rwanda mai kaso 97, sai Malawi mai kaso 95 sai kuma Nijeriya dake da kaso 90.

Shugaban gidauniyar Ivor Ichikowitz, ya shaidawa Xinhua cewa, sakamakon rahoton ya nuna cewa, an amince da manufar kasar Sin ta kara zuba jari a nahiyar. Ya ce idan an saurari ikirarin Amurka da tarayyar Turai na cewa kasar Sin ba za ta amfanawa ci gaban Afrika ba, to matasan nahiyar sun bayyana akasin hakan.

Rahoton ya kuma nuna cewa, matasa na ganin kyakkyawan tasirin da kasar Sin ke yi wajen zuba jari da raya ababen more rayuwa. Sun kuma zabi kasar Sin a matsayin mai bayar da rance da tallafawa tattalin arziki da samar da damarmakin ayyukan yi. Matasan sun kara da cewa, kasar Sin na samar da damarmakin fitar da kayayyakin nahiyar, haka kuma tana samar da kayayyaki masu rahusa. (Fa’iza Mustapha)