logo

HAUSA

Yaushe Amurka za ta cika alkawarin da ta yiwa kasar Sin?

2022-06-15 11:30:14 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasar kwamitin kolin JKS kuma darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin Yang Jiechi ya gana da mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan tsaron kasa Jake Sullivan a Luxembourg a Litinin da ta gabata har na tsawon awoyi hudu, inda suka yi tattaunawa mai zurfi, tare kuma da amincewa da tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu wato Sin da Amurka suka cimma.

Yanzu huldar dake tsakanin sassan biyu ta gamu da matsala, sakamakon kasa tabbatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, duk da cewa, kasar Sin ta nuna sahihanci kuma ta himmantu matuka kan aikin.

An lura cewa, ba zai yiyu a kyautata huldar dake tsakanin Sin da Amurka bisa kokarin da kasar Sin take yi ita kadai ba, yanzu haka Amurka wadda ta saba da tunanin nuna fin karfi tana lalata huldar ta hanyar da take so.

Kwanan baya tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka mai  shekaru 99 Henry Kissinger ya zanta da manema labaran jaridar “The Sunday Times”, inda ya bayyana cewa, bai kamata Amurka ta bukaci kasar Sin ta dace da ma’auni ko al’adu na kasashen yamma ba, abu mafi muhimmanci yayin da ake kokarin raya huldar dake tsakanin Sin da Amurka shi ne, tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma. Kuma abun da ya fi jan hankulan al’ummun kasa da kasa shi ne, yaushe Amurka za ta cika alkawarin da ta yiwa kasar Sin wato ba za ta yi yakin cacar baka, da sauya tsarin kasar Sin, da adawa da kasar Sin, da goyon bayan ‘yancin kan Taiwan, da kuma tayar da rikicin dake tsakaninta da kasar Sin ba. (Jamila)