logo

HAUSA

Takara Tsakanin Jam’iyyun Siyasa, Mummunan Mafarki Ne Na Amurka

2022-06-15 21:20:28 CMG Hausa

Nolan Higdon, kwararren dan jaridan kasar Amurka ya bayyana a kwanan baya cewa, idan kasar Amurka ba ta daidaita manyan batutuwan da ke yin barazana ga demokuradiyya ba, to, taron sauraren ra'ayin jama'a dangane da batun kutsen da aka yiwa ginin majalisar dokokin kasar na Capitol ba zai haifar da da’a mai ido ba.

Jiya Talata ne kwamitin bincike na musamman na majalisar wakilan Amurka ya shirya tarukan sauraren ra'ayin jama'a guda 2 dangane da batun kutsen na ginin Capitol. Ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2021, dubban magoya bayan Shugaba Donald Trump na wancan lokaci, suka kutsa kai cikin babban ginin majalisun dokokin Amurka, a yunkurin canza sakamakon babban zaben kasar ta hanyar nuna karfin tuwo, inda a karshe dai mutane 5 suka rasu yayin da ‘yan sanda fiye da 140 suka jikkata, tare da kama mutane fiye da 700. An bayyana lamarin da ya girgiza duniya a matsayin lokaci mafi muni a tarihin demokuradiyyar Amurka. Ga alama, yadda magoya bayan Trump ba su ji dadin sakamakon babban zaben ya haddasa lamarin, amma hakika Amurka ta dade tana fuskantar rarrabuwar kawuna a cikin gida, da tsanantar matsalar siyasa.

Duk da haka ‘yan siyasan Amurka ba su nemi warware matsalolin daga tushe ba, inda suka ci gaba da ta da rikici dangane da dakile yaduwar annoba, sa kaimi kan bunkasar tattalin arziki, shirin dokar shekarun mallakar bindiga da dai sauransu.

Ana daidaita hakikanin batutuwa ta hanyar demokuradiyya, a maimakon ambaton demokuradiyya a baka kawai. Idan har za a iya samun nasarar dakile yaduwar annoba, hana hauhawar farashin kaya, sanya dokar shekarun mallakar bindiga, da biyan bukatun al’umma ta hanyar demokuradiyya ba, to, ma iya cewa, demokuradiyya ta gamu da mummunar matsala. (Tasallah Yuan)