logo

HAUSA

Shiru-Shiru Ba Tsoro Ba Ne…

2022-06-15 19:36:05 CMG Hausa

A duk lokacin da aka kira taruka kama daga na tattalin arziki, al’adu, ko wasanni ko Ilimi ko kare muhalli ko harkar tsaro, walau a mataki na kasa ko shiyya ko kasa da kasa, muhimman abubuwan da mahalarta tarukan ke tattaunawa, su ne matsaloli da nasarori da aka cimma a wadannan fannoni, gami da sabbin dabaru ko matakai da aka bijiro da su don inganta su, wadda daga karshe za su taimaka wajen haifar da kyakkyawan sakamako da ma burin da ake fatan cimmawa, wanda zai amfani duniya baki daya.

Sai dai wani abin mamaki shi ne, yayin taron tsaro na Shangri-La karo na 19 da ya gudana a kasar Singapore, maimakon a mayar da hankali kan yadda za a inganta matakan tsaro da zai amfani duniya baki daya, sai Amurka da wasu kawayenta suka mayar da hankali kawai wajen neman shafawa kasar Sin baken fenti da ma tsoma baki a harkokin cikin gidanta. Wannan ya sa ministan tsaron kasar Sin Wei Fenghe, yayin da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron, ya nunawa masu irin wannan mugun nufi kan kasar Sin cewa, shiru-shiru fa ba tsoro ba ne...

Sakon da minista Wei ya gabatar, ya kara tunatar da bangaren Amurka da ma duniya baki daya cewa, yanzu huldar da ke tsakanin kasashen 2 tana cikin wani muhimmin lokaci, kuma kyakkyawar huldar da ke tsakaninta da Amurka ta dace da muradunsu da ma duniya baki daya.

Amma idan har Amurka ta nace da neman tayar da rikici tsakaninta da Sin, to hakan ba zai kawo musu da ma kasashen duniya alheri ba. Haka kuma bai dace ba Amurka da kawayenta su rika ayyana kasar Sin a matsayin wai mai takara da Amurka ko barazana, idan kuma suka yi hakan, hakika za ta yi mummunan kuskure. Idan kunne ya ji, to gangan jiki ya tsira.

Kasar Sin dai ta bukaci Amurka da ta daina shafa mata kashin kaji, da neman dakile ci gaban ta, kana ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma illanta muradun kasar Sin. Wani muhimmin batu da Amurka da sauran masu neman ballewar yankin Taiwan ya dace su fahimta da kunnen basira shi ne, sake hadewar Taiwan da babban yanki cikin lumana, shi ne babban fatan al'ummar Sinawa. Kuma duk wanda ya kuskura ya nemi tayar da batun ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, kasar Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da duk wani martani ko ta halin kaka. Domin yaro bai san wuta ba, sai ya taka.

Masu fashin baki na kara jaddada cewa, wajibi ne Sin da Amurka su tattauna da juna, su mutunta juna, su kuma zauna tare cikin lumana, su hada kansu domin samun moriyar juna, amma idan Amurka ta nemi yin fito-na-fito da Sin, to, kasar Sin ta sha nanata cewa, ba za ta yarda a yi mata sakiyar da babu ruwa ba. (Ibrahim)