logo

HAUSA

Kungiyar cinikayyar Afrika zata yi amfani da kudaden cikin gida don bunkasa kasuwanci

2022-06-15 11:20:27 CMG Hausa

Yarjejeniyar kasuwanci cikin ‘yanci ta nahiyar Afrika wato AfCFTA, ta sanar da cewa, zata mayar da hankali wajen karfafa amfani da kudaden cikin gidan kasashen nahiyar domin bunkasa hada-hadar kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika.

Prudence Sebahizi, babban jami’i mai bayar da shawarwari kan tsare-tsare a sakatariyar AfCFTA, ya bayyanawa ‘yan jaridu a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, a halin yanzu galibin hada-hadar kasuwancin da ake gudanarwa tsakanin kasashen Afrika ana amfani ne da dalar Amurka.

A watan Janairun shekarar 2021, an fara gudanar da harkokin kasuwanci karkashin yarjejeniyar AfCFTA, da nufin samar da yarjejeniyar kasuwanci marar shinge mafi girma a duniya, ta fuskar yawan kasashe mahalarta, wanda kuma ya kumshi yawan jama’ar da ta kai biliyan 1.3.

Kawo yanzu dai, kasashe 43 daga cikin kasashen Afrika 55 sun amince da shiga yarjejeniyar cinikin a tsakanin kasashen nahiyar.

Sebahizi ya ce, yarjejeniyar kasuwancin ta yi hadin gwiwa da bankin shigi da fici na Afrika wato (Afreximbank), domin samar da wani tsarin biyan kudade wanda zai karfafa amfani da kudaden cikin gidan kasashen Afrika a hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar.

Ya kuma bayyana cewa, an fara gwajin amfani da kudaden cikin gidan a harkokin cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar, inda aka fara da kasashe shida na yammacin Afrika.

Sebahizi ya kara da cewa, aikin gwajin yana gudanar yadda ya kamata, kuma jimillar kasashen Afrika 20 ne suka nuna sha’awar shiga tsarin biyan kudaden da nufin bunkasar amfani da kudaden cikin gida.(Ahmad)