logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasar Mali

2022-06-14 11:07:21 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya, su samar da taimako mai inganci ga kasar Mali.

Zhang Jun ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD kan Mali da aka yi jiya cewa, yanayin da kasar Mali ke ciki na da sarkakiya.

Ya ce wajibi ne kasashen duniya su taimakawa kokarin Mali na yaki da ta’addanci. Yana mai cewa, ya kamata a mayar da hankali kan bukatar shawo kan dukannin kalubalen yaki da ta’addanci da Afrika ke fuskanta da taimakawa gwamnatin Mali ta fuskar kudi da kayayyakin aiki da bayanan sirri tare da kuma girmama ’yancin kasar na hadin gwiwar tsaro da wasu bangarorin waje.

Game da batun kare hakkin dan Adam da aka ambata a wasu kasashe kuwa, Zhang Jun ya nanata matsayar kasarsa. Yana mai cewa, ya kamata ayyukan yaki da ta’addanci su girmama tare da kare hakkin dan adam. Kana tana adawa da nuna fuska biyu kan batun yaki da ta’addanci da kuma yunkurin siyasantar da batun kare hakkin dan adam.

Ya kara da cewa, kasar Sin na maraba tare da karfafa gwiwar ci gaba da tuntuba tsakanin gwamnatin Mali da kungiyar ECOWAS, ta yadda za a fadada cimma matsaya da cimma yarjejeniyar kan batutuwan da suka shafi mika mulki da za su kai ga dage takunkuman da aka kakabawa Malin tare da samun damar komawa cikin kungiyar da wuri. (Fa’iza Mustapha)