logo

HAUSA

Nijeriya na burin game kaso 70 na kasar da babbar kafar sadarwar yanar gizo zuwa 2025

2022-06-14 11:42:16 CMG Hausa

Mininstan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nijeriya, Isah Pantami, ya ce zuwa shekarar 2025, gwamnatin Nijeriya na da burin samar da babbar kafar sadarwar intanet ta Broadband a kaso 70 na fadin kasar.

Da yake jawabi yayin taron sadarwa a Abuja babban birnin kasar a jiya, ministan ya ce babbar kafar sadarwar ta Broadband, ita ce kashin bayan raya tattalin arzikin zamani ta hanyar amfani da intanet.

Ya ce a cikin rubu’in farko na bana, mamayar babbar kafar sadarwar a fadin kasar ta tsaya ne a kan kaso 42.27, kuma gwamnati na duba bangarorin da za ta inganta, domin ta zarta adadin kaso 70 da take son cimmawa zuwa shekarar 2025.

Ya ce kowa na sane da cewa babbar kafar sadarwar ita ce ke taimakawa raya tattalin arziki na zamani ta intanet, kuma mayar da hankali kan bangaren zai inganta tare da baza komar tattalin arzikin kasar.

A cewarsa, gwamnatin na shawo kan wasu kalubalen da ke fuskanta wajen fadada kafar sadarwar, ciki har da maimaicin biyan haraji da ka’idoji da kuma wahalar samun izini. (Fa’iza Mustapha)