logo

HAUSA

Babbar Kasa Ita Ce Ke Dinke Baraka Ba Kawo Rarrabuwar Kawuna Ba

2022-06-14 17:07:39 CMG Hausa

Yayin taron Shangri-La, da ministocin tsaron kasashen yankin Asiya ke muhawara kan muhimman kalubalen tsaro da yankin ke fuskanta tare da gabatar da dabarun shawo kansu, sakataren tsaron Amurka Lloyd J. Austin III ya tabo wasu batutuwa da suka shafi kasar Sin. Ya ce a baya-bayan nan, ana samun matsi daga rundunar sojin kasar Sin a yankin tekun kudancin kasar. Sai dai rahotanni sun nuna cewa, sama da jiragen ruwa 100,000 ne ke zirga-zirga a tekun a kowacce shekara, kuma babu wanda ya taba fuskantar barazana. Tabbas kasar Sin ba ta takalar fada, sai dai mayar da martani idan aka takale ta. Don haka, duk wani wanda zai yi korafi game da fuskantar barazana daga rundunar sojin kasar Sin, to takalarta ya yi ko keta dokokin, domin Sin ba ta daukar wargi.

Ya kara da cewa, ba su sauya matsayarsu kan manufar kasar Sin daya tak a duniya da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma ba, amma kuma za su ci gaba da taimakawa Taiwan zama mai dogaro da kanta a fannin tsaron kai. Shin me hakan ke nufi? Duk wanda ya amince da ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak da gaske, ya san cewa bai halarta ya yi wata hulda ta kai tsaye da yankin Taiwan ba. Ikirarin taimakawa Taiwan ta fuskar tsaro, ya nuna karara cewa, Amurka na goyon bayan masu neman ballewar yankin, abun da Sin ta sha nanata cewa ba mai yuwuwa ba ne. Kuma a matsayinta na mai wakiltar baki daya Jamhuriyar kasar Sin, batun tsaron Taiwan, hakki ne na kasar Sin, ba wata kasar waje ba.  

Amurka na ikirarin ta damu da tsaron yankin Asiya. Idan har da gaske take, ganin cewa dukkan kasashen yankin na da cikakken iko da yankunansu, kamata ya yi a yi la’akari da bukatun da damuwar kowacce kasa. Kamata ya yi a girmama ’yancin kasashen yankin da hanyoyin ci gaba ko tafiyar da mulki ko na tabbatar da tsaro da suka zabarwa kansu. Bai dace wata kasa ta yi kokarin kakkaba tsarinta a kan wata ba, domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.

Har ila yau, ya ce matsayin babbar kasa na nufin daukar babbar nauyi. Sai dai sam wannan suna ba ta dace da Amurka ba. Babbar kasa ita ta san ya kamata, ita ke dinke baraka idan ta bullo, ba rura wutar rikici ba, ita ke hade kan al’umma ba kawo rarrabuwar kawuna ba. (Fa’iza Mustapha)