logo

HAUSA

Labarin dan kasar Angola mai tallata abincin kasar Sin

2022-06-14 14:25:16 CMG Hausa

Norvan Romario Luemba, dan asalin kasar Angola ne dake kudu maso yammacin nahiyar Afirka, wanda ya shafe shekaru 7 yana zaune a kasar Sin. Yanzu yana aikin tallata abinci kala-kala na sassa da dama na kasar Sin a shafinsa na sada zumunta, abun da ya sa ya kara fahimtar al’adun dake tattare da abincin kasar.

“Dan uwa, me ya sa wannan abinci yake da dadi haka? Ban taba ci ba.”

Norvan Romario Luemba ya wallafa hotunan bidiyo da dama a shafinsa na sada zumunta don tallata abinci kala-kala masu dadi na kasar Sin, al’amarin da ya jawo masa mabiya kusan miliyan 4.

Norvan ya zo kasar Sin ne karatu a shekara ta 2015, inda ya bayyana cewa:

“Yanzu shekaru na 7 a kasar Sin, na fara zuwa ne don yin karatu. Na yi karatu a wata jami’a da ake kira Huaqiao University a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudancin kasar Sin, kuma fannin da na karanta shi ne ilimin sadarwa.”

Kamar sauran wasu baki ‘yan kasashen waje, kafin isowarsa kasar Sin, Norvan ba shi da masaniya sosai game da kasar, kuma abin da kawai ya sani game da kasar Sin, shi ne shirin talabijin na zamanin da na kasar.

Norvan ya bayyana cewa:

“A wancan lokaci, ina sha’awar kallon wani shirin TV na kasar Sin mai suna ‘Princess Huanzhu’, wanda ya samu karbuwa sosai a kasata Angola. Da karfe 8 na daren kowace rana, mutane su kan kalli shirin, abun da ya sa nake tunanin cewa, kowane dan kasar Sin ya iya wasan Kungfu. Sannu sannu na fara sha’awar al’adun kasar Sin.”

Norvan ya ji dadin karatu da zama sosai a birnin Xiamen. Bayan da ya gama karatu, ya zabi wani birni na daban don ya ci gaba da zama, wato Shenzhen. Saboda matukar kaunar abincin Sin, Norvan ya fara aikin tallata abincin a kafofin sada zumunta daban-daban ta yanar gizo. Abincin kasar Sin yana kunshe da al’adun kasar da dama, a cewar Norvan, sakamakon kara nazarin abinci da mutanen kasar suke yi, mutane daga sassa daban-daban na kasar Sin za su iya bullo da abinci masu dadi kala-kala.

A birnin Liuzhou na jihar Guangxi dake kudancin kasar Sin, Norvan ya dandana wani nau’in taliyar shinkafa mai dandano na musamman, da ake kira Luo Si Fen. A birnin Lanzhou na lardin Gansu dake yammacin kasar kuma, ya samu damar dandana shahararren abincin wurin, mai suna Niurou Mian, wato taliya hade da naman saniya. A lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, Norvan ya ci wani nau’in taliya mai yajin gaske. Da farko ya ji tsoro, amma sakamakon kwarin-gwiwar da mai sayar da abinci ya ba shi, Norvan ya gwada har ya fara kaunar wannan taliya. Yanzu yana kokarin tallata abincin kasar Sin kala-kala ga duk fadin duniya.

Norvan ya bayyana cewa, ya gamu da mutanen kasar Sin da yawa da suka burge shi, a yayin da yake tafiye-tafiye a sassa daban-daban na kasar. Akwai mabiyansa a kafafen yada labarai, da suke son daukar hoto tare da shi, akwai kuma masu sayar da abinci da suka ba shi abinci kyauta don ya dandana, duk wadannan sun burge Norvan kwarai da gaske, inda ya ce, irin kirkin da mutanen kasar Sin suka nuna masa, ya sa ya ji dadi kamar yana gida. Norvan ya ce:

“Wata rana bayan na gama daukar shirin bidiyo a wani gidan cin abinci, na je zan biyan kudi, sai mai gidan ya ce ba sai na biya ba, na tambaye shi dalili. Ya ce, ni ne bako dan kasar waje na farko da na ci abinci a wajensa, don haka yana so ya gayyace ni cin abinci. Gaskiya irin kirkin da ya min, ya faranta min rai sosai.”

Norvan ya ce, Sin kasa ce mai dimbin al’adu, kuma abincin kasar na tattare da al’adu iri daban-daban. Daga abinci kala-kala, za’a iya fahimtar ci gaban tarihi, da na rayuwar al’ummomin kasar a fannoni da dama.

Norvan ya ce:

“Daga abinci mai dadi, za’a iya fahimtar hikima da kwazon aiki na wanda ya dafa shi, haka kuma ya bayyana sauyin zamani na kasar Sin. Alal misali, mutanen dake jihar Mongoliya ta gida dake arewacin kasar, a baya, makiyaya ne, inda suka kawo sauye-sauye ga abincinsu, don ya dace da yanayin zama wurin, al’amarin da ya shaida tarihin rayuwa gami da al’adunsu.”

A lokacin da ya waiwayi rayuwarsa har na tsawon shekaru 7 a kasar Sin, Norvan ya ce, a duk lokacin da ya iso nan, ya kan fahimci cewa, ashe ainihin rayuwar mutanen kasar ta bambanta kwarai da gaske da irin rayuwar da yake tunani a baya. Ya ce yanzu ya kusan zama “rabin dan kasar Sin”, saboda ya riga ya saba da yin sayayya ta kafar yanar gizo, duba da ingantaccen tsarin biyan kudi ta intanet da na jigilar hajoji na kasar. Norvan ya ce, yana jin dadin sayayya ta kafar intanet, saboda hakan ba ya bata masa lokaci, inda ya ce:

“Rayuwar mutanen kasar Sin akwai saukin matuka. Duk inda ka je, in dai kana da wayar salula, za ka iya biyan kudi da ita, ba tare da amfani da katin banki ko tsabar kudi ba. Na kan sayi abinci, ko yin odar abinci a gida ta kafar intanet cikin sauki, gaskiya ina jin dadi. Harkokin sufuri ma yana da sauki sosai, ina jin dadin tafiya cikin jirgin kasa mai saurin gudu da jirgin dake karkashin kasa wato subway, akwai sauri sosai.”

Game da shirin da yake da shi a nan gaba kuwa, Norvan ya ce, burinsa da kasar Sin a hade suke:

“Ina da wasu burika guda uku. Na farko, ina so in kafa kasuwanci na kaina. Na biyu ina so na samu katin zaman dan kasar Sin, wato green card. Na uku, ina fatan kafa iyali a nan. Zan yi bakin kokarina don cimma wadannan burika, ina da yakinin cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu.” (Murtala Zhang)