logo

HAUSA

Yara ’yan kwadago da ke kasar Amurka wadda ke ikirarin kare hakkin dan Adam

2022-06-14 11:01:32 CMG Hausa

A karkashin hasken rana mai zafin gaske, wani yaro dan shekaru 7 da haihuwa ya dukufa kan aikin gona. Wa zai iya alakanta batun da kasar Amurka, wadda ta fi ci gaban tattalin arziki, kuma a kullum ke daukar kanta a matsayin misali wajen kare hakkin bil Adam? Sai dai wani hoton da kungiyar ’yan kwadagon gandayen noma na kasar Amurka ta fitar ta shafin sada zumunta a bara ya tabbatar da cewa, hakan na faruwa dai a wannan kasa.

Tuni yau shekaru sama da 100 da suka wuce, aka fara daukar yara ’yan kwadago aiki a mahakar kwal da gandayen noman ganyen tabar sigari da masaku na kasar. Abin bakin ciki shi ne, duk da ci gaban da ’yan Adam suka samu ta fannin wayewar kai cikin shekarun 100 da suka wuce, har yanzu ana yawan samun yara ’yan kwadago a kasar Amurka.

Musamman a fannin aikin noma, yara ’yan kwadago na kasar ta Amurka sun haifar da damuwa idan aka yi la’akari da yanayin da suke ciki. Bisa kididdigar da kungiyar shirin horar da ’yan kwadagon gandayen noma ta kasar Amurka ta yi, an ce, yanzu haka akwai yara ’yan kwadago kimanin dubu 500 a kasar, kuma da yawa daga cikinsu sun fara aiki tun lokacin da suke da shekaru 8 da haihuwa, kuma suna aiki na tsawon sa’o’i 72 a kowane sati. Har wa yau, yaran sun dade suna aiki a muhallin dake da sinadarai masu guba. Lamarin da ya sa suke yawan kamuwa da cutar sankara. Ban da haka, sabo da yadda suke aiki da na’urorin noma masu nauyi da kuma kaifi, ba tare da samun horon kariya da suka kamata ba, ya sa su kan fuskanci hadari a lokacin aiki. Rahoton da jaridar “Washington Post” ta samar ya yi nuni da cewa, daga shekarar 2003 zuwa ta 2016, akwai yara ’yan kwadago 452 da suka mutu a kasar, kuma sama da rabinsu suna aiki ne a gandayen noma.

A bara, masana’antu da dama da ke jihar Wisconsin ta arewacin kasar Amurka sun fuskanci matsalar karancin ’yan kwadago. Don taimaka musu daidaita matsalar, majalisar dokokin jihar ta mai da hankalinta kan yara, inda a watan Oktoban bara, majalisar dattawa ta jihar ta zartas da shirin dokar tsawaita lokacin aiki na ’yan kwadago da ba su balaga ba.

A hakika, bisa yarjejeniyar hakkin yara ta MDD, dole ne a kare hakkin yara, amma sakamakon yadda kasar Amurka ta ki amincewa da yarjejeniyar, inda ta zama kasa daya tilo a duniya da ba ta amince da ita ba, ya sa yaran kasar ba su iya samun kariya daga yarjejeniyar.

A watan Yunin shekarar 2002, a yayin babban taron kwadago na kasa da kasa karo na 90 an tabbatar da ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin “ranar hana yara kwadago ta duniya”, don yin kira ga kasa da kasa da su mai da hankali a kan batun yara ’yan kwadago. Amma yaushe ne za a kai ga mayar da yarantar da ta kamata ga yaran kasar a matsayin “misalin kare hakkin dan Adam?” (Lubabatu Lei)