logo

HAUSA

Mutane 50 sun rasu sakamakon harin da aka kai yankin arewacin Burkinafaso

2022-06-14 10:32:34 CMG Hausa

Kakakin gwamnatin kasar Burkinafaso Lionel Bilgo, ya bayyana jiya Litinin cewa, akalla fararen hula 50 sun rasa rayukansu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai yankin Sahel dake arewacin kasar a daren ranar 11 ga wata.

Bilgo ya kara da cewa, dakarun da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari garin Seytenga na jihar Seno dake yankin Sahel a daren ranar 11 ga wata, inda zuwa yammacin jiya Litinin, aka samu akalla fararen hula 50 da suka rasu, yana mai cewa akwai yiwuwar adadin zai karu a nan gaba, kana harin ya sa mazauna da dama tserewa daga garin. (Jamila)