logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a harin Seytenga a Burkina Faso ya kai 79

2022-06-14 20:39:58 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu sanadiyar harin da aka kai a karshen mako a yankin Seytenga da ke yankin Sahel na kasar, ya karu daga 50 zuwa 79.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar na nuna cewa, a yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro da bincike, an kuma gano wasu sabbin gawarwaki 29, wanda ya kawo adadin na wucin na wadanda harin ya rutsa da su zuwa 79

Harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai a gundumar Seytenga da ke lardin Seno a arewacin Burkina Faso, ya faru ne cikin dare tsakanin Asabar da kuma Lahadi. Sabon shugaban kasar Laftana Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ya ayyana zaman makoki a fadin kasar na sa'o'i 72 daga yau Talata zuwa ranar Alhamis.(Ibrahim)