logo

HAUSA

Samun ci gaba na bukatar hangen nesa

2022-06-13 18:08:15 CMG Hausa

Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya ya yi jawabi na musamman a jiya ranar Dimokuradiya, inda ya jaddada alkawarin tabbatar da tsaro a kasarsa. Kana a nasu bangare, jama’ar kasar sun ci gaba da nuna damuwa kan matsalolin rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa, a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana koma bayan tattalin arziki a matsayin babban dalilin da ya haddasa rashin kwanciyar hankali a wasu wuraren kasar.

Abin lura shi ne, ba Najeriya ce kadai ke fuskantar matsalar tattalin arziki ba. A halin yanzu, annobar COVID-19 da yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, sun jefa tattalin arzikin duniya cikin wani yanayi na rashin tabbas. Idan muka dubi alkaluman da aka samu a kwanakin nan, za mu ga jimillar GDP ta kasar Amurka ta ragu da kaso 1.4, sa’an nan yadda bankin tsakiya na kasar ya dauki matakai don daidaita matsalar hauhawar farashin kayayyaki, ya sa kasuwar hannayen jari ta kasar ta gamu da babbar matsala, inda farashin kusan dukkan hannayen jari ya ragu sosai. Yayin da a kasar Birtaniya, hauhawar farashin kayayyaki ta sa bankin Ingila ya daga jimillar ruwan da ake bayar kan kudin ajiya zuwa wani matsayin da ba a taba ganin irinsa ba cikin wasu shekaru 13 da suka wuce, tare da sanar da tabarbarewar tattalin arzikin kasar. A cikin wannan yanayi mai wuya da ya shafi dukkan kasashe, ya kamata a yi kokarin yin hangen nesa, da daukar nagartattun matakai, da hadin gwiwa da sauran kasashe yadda ake bukata.

Dole ne a magance matakai na son kai, da ma rashin hangen nesa. Misali, a Najeriya, wasu matasa sun dauki makamai sun zama ‘yan fashi sakamakon kwadayi. Amma idan ana da hangen nesa, za a iya ganin cewa ayyukan da suke yi sun haifar da barna ga jama’a, kana nan gaba tabbas za a yanke musu hukunci bisa muggun ayyukan da suka aikata. Ban da wannan kuma, misali a kasar Amurka, gwamnati ta bari cutar COVID-19 ta haddasa asarar rayukan mutane fiye da miliyan 1, da raunana tattalin arziki, tana neman raya tattalin arzikin kasar ta hanyar zuba makudan kudi cikin kasawanni kawai amma ba tare da daukar matakai na hana bazuwar annoba ba, abun da ya sa ake fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a kasar. Sa’an nan, wasu kasashen yammacin duniya, yayin da suke fuskantar koma bayan tattalin arziki, suna neman ta da rikici tsakanin sauran kasashe, da raunana tattalin arzikinsu, don neman sanya karin jari komawa cikin kasuwannin gida. Amma a hakika, bayan an samu barkewar yaki a wani yanki, lamarin ya kan kawo cikas ga aikin samar da kayayyaki na duniya, da haifar da illa ga tattalin arzikin kasashe daban daban.

Dalilin da ya sa kasar Sin ke iya samun ci gaban tattalin arzikinta cikin matukar sauri, cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, shi ne domin hangen nesa da ta yi, abin da ya sa take iya daukar nagartattun matakai masu dorewa, da daidaita moriyarta da ta sauran kasashe. Yayin da take hulda da kasashen Afirka, kasar Sin ta tsayawa kan manufar “tabbatar da daidaito, da moriyar dukkan bangarori”. Tana fatan ganin kasashen Afirka sun samu ci gaban tattalin arizki, kana tana goyon bayan hadin gwiwar da kasashen Afirka suke yi da sauran kasashe. Idan mun dauki bashin da kasar Sin ta ba kasashen Afirka a matsayin misali, za mu ga cewa, ko da yake kafofin watsa labaru na kasashen yamma su kan bayyana shi a matsayin “mulkin mallaka” da “tarkon bashi”, a hakika kasar Sin na ba da bashi ne bisa ainihin bukatun da kasashen Afirka suke da shi, da taimakawa kasashen Afirka inganta kayayyakin more rayuwa: Tun daga shekarar 2000, kamfanonin kasar Sin sun taimaki kasashen Afirka wajen gina ko kuma inganta layin dogo na fiye da kilomita dubu 10, da hanyoyin mota kimanin kilomita dubu 100, da gadaje kimanin dubu 1, da tashoshin jiragen ruwa 100, dai dai sauransu. Sa’an nan idan wata kasa ta gamu da matsalar biyan bashi, kasar Sin za ta tattauna da ita don samar da wata dabara mai dacewa don daidaita batun, har ma ta kan yafe wa kasa maras karfi bashin da take binta. Hangen nesa ne ya sa kasar Sin take son zuba jari don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, gami da ba da damar samun ci gaban harkoki ga kamfanonin kasar. (Bello Wang)