logo

HAUSA

Mai yiwuwa ne maza ‘yan asalin Afirka masu sanko su kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sankarar mafitsara

2022-06-12 16:48:29 CMG Hausa

Masu nazari da ke aiki a jami’ar Pennsylvania ta kasar Amurka sun kaddamar da wani rahoto a kwanan baya da ke nuna cewa, watakila matsalar sanko da wasu maza ‘yan asalin Afirka suke fuskanta tana da nasaba da karuwar barazanar kamuwa da ciwon sankarar mafitsara, musamman ma wadanda suka fara fuskantar matsalar sankon a lokacin kuruciyarsu. Amma duk da haka, ana bukatar ci gaba da bincike kan lamarin a cikin sauran mutane.

Alkaluman da cibiyar nazarin ciwon sankara ta kasar Amurka ta bayar sun nuna cewa, a kasar ta Amurka, maza ‘yan asalin Afirka sun fi fuskantar barazarar kamuwa da ciwon sankarar mafitsara, kuma yiwuwar kamuwa da ciwon da suke fuskanta ta fi ta maza masu farar fata yawa har sau biyu ko fiye da haka. An yi wannan nazari ne kan maza ‘yan asalin Afirka 537, ciki had da 318 wadanda suke fama da ciwon sankarar mafitsara. Bayan da masu nazarin suka kwatanta nau’o’in sanko da masu sanko suke fama da su da kuma lokacin da suka fara fama da su, sun gano cewa, a takaice, barazanar kamuwa da ciwon sankarar mafitsara da maza masu sanko suke fuskanta ta fi ta marasa sanko da kashi 69 cikin dari. Sa’an nan kuma, barazanar kamuwa da ciwon sankarar mafitsara kafin shekarunsu su kai 60 a duniya da wadanda suka fara yin sanko kafin shekarunsu su kai 30 a duniya sun fi na marasa sanko yawa har sau biyu ko fiye da haka.

Masu nazarin suna ganin cewa, watakila dalilin da ya sa hakan na da nasaba da sinadarin Hormone da jikin dan Adam ke amfani da shi, wato idan wani nau’in Hormone ya yi yawa fiye da kima a jikin namiji, wannan namiji zai yi samun sanko, kana kuma hakan ya kan haddasa matsalar mafitsara ga maza tsoffafi.

Manazartan sun bayyana cewa, an yi wannan nazari ne a kan Amurkawa maza ‘yan asalin Afirka kawai. Kuma a nan gaba za su fadada nazarinsu kan sauran mutane. An dai buga wannan rahoton nazari ne a kan mujallar wata-wata mai suna “nazari kan ciwon sankara, alamun kamuwa da ciwon a jikin mutum, da yin rigakafin kamuwa da ciwon”, wadda cibiyar nazarin ciwon sankara ta kasar Amurka ta wallafa.