logo

HAUSA

Adadin wadanda suka kamu da cutar kyandar biri a Najeriya ya karu zuwa 31

2022-06-12 15:54:02 CMG Hausa

              

Wani rahoton da hukumomin lafiya suka fitar a kasar Najeriya na cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar kyandar biri a kasar, ya karu zuwa 31, yayin da aka samu karin mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan kasar dake zama mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

A cikin rahotonta na baya-bayan nan game da cutar, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce, daga watan Janairu zuwa wannan lokaci, kasar ta samu adadin mutane 110 da ake zargi sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da mutane 31 da suka kamu da cutar daga jihohi 12.

Rahoton ya ce, an kaddamar da cibiyar gudanar da ayyukan ba da agajin gaggawa ta kasa a watan Mayu, sakamakon tantance hadarin da aka gano, wanda ya jefa Najeriya cikin hadarin barkewar cutar ta kyandar biri.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, bullar cutar kyandar biri kwatsam a kasashe da dama na duniya ya nuna cewa, cutar ta dade tana yaduwa a wajen kasashen yammaci da tsakiyar Afirka, inda galibi ake samun ta.(Ibrahim)