WHO: matsalar kiba da nauyin da ya wuce kima yana karuwa a Afrika
2022-06-12 16:50:22 CMG Hausa
Ofishin hukumar lafiya ta duniya WHO a nahiyar Afrika ya bayyana a kwanan baya cewa, mutum guda cikin mutane biyar manya da kuma yaro guda cikin yara da matasa 10 a kasashe 10 na Afrika da ke fuskantar matsalar kiba za su iya gamuwa da matsalar nan da watan Disambar shekarar 2023, matukar aka gaza daukar kwararran matakan magance faruwar lamarin.
Hukumar WHO ta bayyana cikin alkaluman da ta fitar na baya-bayan nan gabannin murnar ranar matsalar kiba ta kasa da kasa, wato ranar 4 ga watan Maris na kowace shekara cewa, yawan baligai wadanda suke fama da matsalar kiba zai kai kashi 13.6 zuwa kashi 31 cikin kashi 100 a kasashen Afrika 10 da ke fama da matsalar, yayin da yawan yara da matasa masu fama da matsalar kiba zai kai kashi 5 zuwa kashi 16.5 bisa dari 100.
Madam Matshidiso Moeti, darektar hukumar WHO a nahiyar Afrika ta bayyana cewa, Afrika tana kara fuskantar karuwar matsalar kiba da nauyin da ya wuce kima, kuma matsalar tana dada kamari. Wannan matsalar tamkar wani bam ne dake jiran lokaci. Muddin ba a dauki matakai ba, to, miliyoyin mutane ciki har da yara kanana, za su fuskanci barazanar raguwar tsawon lokacin rayuwa sakamakon matsalar kiwon lafiya.
Ana danganta batun nauyin da ya wuce kima da wasu cututtuka masu tsanani, kuma akwai bukatar a bincika alakar da ke tsakanin batun da kuma wadanda suke kwanta a asibiti sakamakon kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Sai dai har yanzu babu wasu takamammun alkaluma dangane da nahiyar ta Afrika, amma a wani rahoton binciken da aka wallafa a mujjalar “cututtuka masu yaduwa da kiwon lafiyar al’umma”, an gano cewa, an samu hasarar rayukan mutane miliyan 2.5 sakamakon cutar COVID-19 a duk duniya ya zuwa karshen watan Fabrairun shekarar 2021, wasu mutane miliyan 2.2 daga cikinsu ne suke zama cikin kasashen da ke da adadin sama da kashi 50 bisa kashi 100 na yawan al’ummarsu dake fama da matsalar nauyin jiki da ya wuce kima.
Wani shiri na kasa da kasa wanda ke samun tallafin hukumar WHO, da wasu kungiyoyin kasa da kasa, yana tallafawa kasashen Kenya, da Tanzania, da kuma Uganda, wajen tsara da kuma aiwatar da ka’idojin sa ido da matakan harkokin kudi, a kokarin kara azama kan ci abinci ta hanyar da ta dace da kuma motsa jiki yadda ya kamata.
Kamar dai yadda sanarwar hukumar WHO ta bayyana, ya zuwa shekarar nan ta 2022, hukumar WHO za ta yi aiki tare da karin kasashen Afrika 10 wadanda ke fuskantar matsaloli wajen gaggauta gudanar da shirin rage matsalar kiba.(Ahmad)