logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kai wani asibiti a kasar Kamaru

2022-06-12 16:06:24 CMG Hausa

 

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ko OCHA a takaice, ya yi Allah wadai da kakkausar murya, kan harin da aka kai a wani asibiti a yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru mai fama da tashin hankali dake magana da harshen turancin Ingilishi.

Matthias Naab, jami'in kula da ayyukan jin kai na MDD a kasar Kamaru, ya bayyana cikin wata sanarwa jiya Asabar cewa, hare-haren da aka kaiwa ma'aikatan kiwon lafiya, da marasa lafiya da kayayyaki, mummunan take dokokin kare hakkin bil-Adama ne

Yayin da yake karin haske kan harin da aka kai ranar Larabar da ta gabata, lokacin da wasu da ake zargin ‘yan a-ware ne, suka kai hari tare da kona asibitin gundumar Mamfe da ke yankin, ya bayyana cewa, tilas ne a gudanar da bincike a kuma hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

A cewar OCHA, daga watan Janairu zuwa yanzu, an kai a kalla hare-hare guda biyar kan ma'aikatan lafiya.

Sanarwar ta bayyana cewa, an fuskanci yawan hare-hare kan harkokin kiwon lafiya tare da barazana, da sace ko jikkata ma'aikatan kiwon lafiya, ko kuma kashe su tare da lalata kayayyakin kiwon lafiya baki daya, a rikicin da ke faruwa a yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar Kamaru. (Ibrahim)