logo

HAUSA

Jakadan Sin a Saliyo ya halarci taron karawa juna sani tsakanin ofishin jakadancinsa da kungiyoyin sada zumunta ta Sin da Saliyo

2022-06-11 17:46:37 CMG Hausa

A ranar 8 ga wata, ofishin jakadancin kasar Sin dake Saliyo, ya shirya taron karawa juna sani tsakanin ofishin da kungiyoyin sada zumunta ta kasashen Sin da Saliyo na shekarar 2022.

Jakadan kasar Sin a Saliyo, Hu Zhangliang, ya gabatar da muhimmin jawabi game da halin da kasa da kasa ke ciki a halin yanzu, da manufofin bunkasa cigaba na kasar Sin da na diflomasiyyarta, da kuma huldar dake tsakanin Sin da Saliyo. Ya bayyana cewa, kasar Sin ta kara kaimi tare da samar da gagarumin taimako ga zaman lafiya da cigaban duniya. Yadda  kasar da ke da al’umma biliyan 1.4 ta bunkasa, wani babban cigaba ne ga bil adama baki daya, ba wai barazana ce ko kuma kalubale ga duniya ba.

Jakada Hu, ya bayyana cewa, duk wani yunkurin bata sunan kasar Sin, da neman lalata huldar dake tsakanin Sin da Saliyo da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika ba zai taba samun karbuwa ba. Kasar Sin a shirye take ta cigaba da karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da kasar Saliyo, domin amfanawa bangarorin biyu.

Shugabannin kungiyoyin sada zumunci tsakanin Saliyo da Sin, da kafafen yada labaran kasar ta Saliyo sun bayyana cewa, kasar Sin ta samar da taimako na gaskiya don cigaban kasashen Afrika, cikinsu har da kasar Saliyo, a dogon lokaci, kana zumuncin dake tsakanin Sin da Saliyo, da kuma na Sin da Afrika, ya yi matukar ratsa zukatan al’umma. Duk wani yunkurin neman lalata kimar kasar Sin, da neman lalata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Saliyo ba zai taba samun nasara ba.(Ahmad)