logo

HAUSA

Rahoton karya da Adrian Zenz ya watsa ya tona asirin Amurka

2022-06-10 21:01:51 CMG Hausa

Wata doka mai suna wai hana tilastawa ‘yan Uygur aiki ta Amurka za ta fara aiki nan bada jimawa ba. Kwanan nan, Adrian Zenz, wanda ya sha kitsa karairayi ya sake fitar da wani rahoton dake nuna cewa, wai kasar Sin na kara tilastawa mutane aiki. Irin wannan doka tana cike da karairayi, wadda ta tona asirin kasar Amurka, na kawar da Xinjiang daga cikin yankuna masu samar da kayayyaki ga duniya.

Hakika, kafofin watsa labarai sun ruwaito maganganun tsoffin ‘yan diflomasiyyar Amurka a kasar Sin dake cewa, babu wata matsala a Xinjiang, dukkanmu mun sani, amma yin amfani da jihar Xinjiang don rura wutar rikici kan batutuwan da suka shafi tilasta yin aiki, da kisan kare-dangi, da kuma keta hakkin dan Adam, dabara ce ta tsunduma gwamnatin kasar Sin cikin mummunan mawuyacin hali. 

Rahoton karya da Adrian Zenz ya fitar a wannan karo, yana cewa, wai duk da cewa shaidun da za’a iya amfani ba su da yawa, amma sabon ci gaban da ake samu, ya sa ake kara tilastawa mutane aiki, har zuwa wasu sana’o’in fasahohin zamani. Amma rahoton bai fayyace wane sabon ci gaba ba ne, kana bai bayyana shaidu da wasu alkaluma ba, illa karya ce zalla kawai.

A karshen bara, gwamnatin Amurka ta sa hannu kan wani shirin doka mai suna wai “hana tilastawa ‘yan Uygur aiki”, wanda za’a fara amfani da ita tun daga ranar 21 ga watan Yunin bana. Dokar za ta hana Amurka shigo da hajojin Xinjiang. Wato ta hanyar fakewa da batun hakkin dan Adam, wannan doka za ta hana ci gaban Xinjiang, da kwace damar samun bunkasuwa na mazauna yankin, kuma wannan take keta hakkin dan Adam ne a Xinjiang.

Kusan makwanni biyu da suka wuce, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi jawabi kan manufofin gwamnatin Amurka game da kasar Sin, inda ya ambaci wasu muhimman kalmomi uku da suka hada da, zuba jari, kulla kawance, da yin takara. Bisa fahimtar Amurka, yin takara shi ne matsa lamba ga abokan takara ta hanyar shafa musu bakin fenti, da kuma keta ka’idojin kasuwancin kasa da kasa, to, abin da mutum ya shuka, shi zai girba. (Murtala Zhang)