logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta ce mayakan ISWAP ne ke da alhakin mummunan harin coci

2022-06-10 10:44:54 CMG Hausa

Gwamnatin Najeriya ta ce tana zargin kungiyar masu tsattsauran ra’ayin addini dake yammacin Afrika wato (ISWAP), da alhakin kaddamar da harin baya bayan nan kan wata coci, a jahar Ondo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, inda aka kashe a kalla mutane 40.

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola, ya fadawa taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, mayakan ISWAP ake zargi da kai harin na cocin St. Francis Catholic dake garin Owo, a jahar Ondo, a ranar Lahadi.

A cewar Aregbesola, ko da yake, hukumomin tsaro suna kokarin murkushe bata garin, amma har yanzu ba su kama ko mutum guda dake da alaka da harin ba.

Ministan ya ce, an umarci hukumomin tsaro da su binciko wadanda suka shirya harin domin hukunta su, inda ya jaddada cewa, harin ba shi da alaka da kabilanci ko addini, sannan ya tabbatar da cewa, kungiyar maso tsattsauran ra’ayi ta ISWAP ba su da alaka da hakikanin addini. (Ahmad)